Halvardeh ko Halva Shekari

Halvardeh ko Halva Shekari, na daya daga cikin alawoyin kasar Iran mai matukar amfani ga jikin dan adam, kuma anayin wannan alawan ne daga markadadden ridi. Halvardeh tana da dandano mai zaki kuma anfi ci da bredi a lokacin karin kumallo.

Gidan tsara mulki

Wannan gida na tsara tsaran mulki na birnin tabriz yana a wannan yanki mai suna azarbaijan wanda yake na gwamnati ne, wannan ginin tsawon shekaru da dama kusan daga shekarar ali dubu daya da dari tara da shida (1906) yazama wurin na shawar wari da duk wanda ke cikin wannan motsi, tarukan na gudana da tsarin mulki na wannan kasa wato Iran.

Godiya al'adar Iraniyawa

Jama'ar Iran na godiya da kyakkyawan kauyen Khaneqah wanda yake a yankin lardin Kermanshah, suna godiya ga Allah daya basu albarkar noman rumman.

​Kogin hoda (Pink lake) ya wuce Yanayi

Mun saba da ganin ruwa a shudi (blue) ko watakila kore-kore (greenish). A nan tafki ne da yazo da yanayi na daban na ruwan hoda. Tafkin Lipar Lake (wanda aka sani da ruwan hoda pink lake) ya samo asali saboda wani abu mai tsabta wanda ke dauke da daruruwan halittun ruwa na planktons a wannan yankin.

Magudanar Ruwa (Natural pesticide waterfall)

Magudanar Ruwa (Natural pesticide waterfall) Magudanar Ruwan Takht-e Soleyman, wanda aka sani da Ab-e Malakh (grasshopper’s water) yana daya daga cikin wurare masu ban-mamaki da aka sani sukai suna sosai a Isfahan, Iran. Ruwan da ke gudana daga Takht-e Soleyman ya ƙunshi wasu sinadirai da suke aiki a matsayin magungunan ƙwari a cikin gonakin yankin.

Hubbaren Bouzar Jomehr Ghaeni.

South Khorasan

Hubbaren Bouzar Jomehr daya daga cikin sanannun sufaye kuma mawaki a karni na hudu zuwa biyar Hijira kamariyya ya kasance ne a nisan kilomita biyar daga Kudancin Qaenat, a zagaye da dutsen Abu-Zar. Bouzar Jomehr Ghaeni ya kasance mawaki daga karni na hudu zuwa farkon karni na biyar hijira kamariyya, wanda basirarsa da hikimarsa suka kawo ci gaban kasar Iran a zamanin mulkin daular Ghaznabiyawa. Tsarin adon da aka yi a karkashin hasumiyar mai gurbi-gurbi ya kasance daya daga cikin bangare mafi kyau a wannan ginin, sannan kuma akwai wata tsohuwar bishiya – mai shekaru 700- a gefensa. Wannan wurin tarihi ya kasance yana janyo hankulan masu yawon bude ido a yankin, saboda kimar wurin. Saman dutsen Qaen, na dauke da hubbaren Zeid al-Nar Afriz, Gadar dutsen Khezri, Sararin kasar Esfadan mai ban mamaki, Yankin Shaskuh mai shuke-shuke da dabbobi na musamman, gidan tarihi kan ilimin samuwar mutum, ruwa da shahararrun abubuwa, soyayyun abinci, gwarzaye da kogunan Noghab, Kabarurrukan Abolmafakher, Robat Zardan da sauransu, duk wadannan suna daga cikin abubuwan tarihi da na dabi’a masu janwo hankula zuwa wannan karamar hukuma. Wannan gini na hubbaren Bouzar Jomehr Ghaeni, an yi masa rajista ne a cikin jerin wuraren tarihi na kasar Iran mai dauke da lambar rajista 2,759, kuma a yanzu haka ginin yana karkashin kulawar cibiyar kula da kayayyakin tarihi da ayyukan hannu gami da yawon bude ido ta kasa.

utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸ utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸ utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸