A Yau Ne Kotu Za Ta Yanke Hukunci Akan Zaben Shugaban Kasa

2019-09-11 10:07:44

A yau Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya za ta yanke hukunci na karshe akan sakamakon zaben da aka yi a watan Febrairu.

Jam’iyyar adawa ta PDP da dan takararta na shugabancin kasa Alhaji Atiku Abubakar, sun bukaci ganin cewa kotun wacce mai shari’a Muhammad Garba yake jagoranta, ta rushe sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda ya bai wa Muhammadu Buhari nasara.

Bugu da kari jami’iyyar ta adawa, tana son ganin an bayyana dan takararta Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben, ko kuma ta bayar da umarni da a sake yin wani zaben

Daya daga cikin lauyoyin jam’iyyar PDP Mike Ozekhome ( SAN) ya ce; A yau Laraba da karfe 9;am za a yanke hukunci. Lauyan ya bayyana fatansa na ganin cewa; Wanda yake wakilta ya sami nasara.

Tags:
Comments(0)