Najeriya: Osinbajo ya kaddamar da wata sabuwar cibiyar sarrafa albarkatun dabbobi

2019-09-11 09:06:31

Mataimakin shugaban kasar ta Najeriya, Prof. Yemi Osinbajo ya kaddamar da cibiyar sarrafa dabbobi ne ta kasa ( NLTP) a gandun dajin gongoshi dake karamar hukumar Mayo-Belwa a jahar Adamawa

Mataimakin shugaban kasar ta Najeriya wanda ya gabatar da jawabi a wurin bikin kaddamar da cibiyar, ya ce; Shirin yana a karkashin tsarin da gwamnatin tarayya ta yi ne na hada kai da jahohi a karkashin majalisar tattalin arziki ta kasa.

Pro Osinbajo ya kara da cewa; Manufar tsarin shi ne bunkasa harkokin kiwo a Najeriya, kuma za a aiwatar da shi a cikin jahohin Adamawa, Benue, Kaduna, Plateau, Nasarawa, Taraba da Zamfara.

Bugu da kari, mataimakin shugaban kasar ya ce; tsarin zai kasance ne a matsayin na hadin guiwa a tsakanin gwamnatin tarayya da jahohi, manoma,makiyaya da masu sha’awar zuba hannun jari.

Har ila yau, mataimakin shugaban kasar ta Najeriya ya ce; gwamnatocin jahohi ne za su bayar da filaye, kuma gwamnatin tarayya ba za ta taba karbar kasa daga jaha ko karamar hukuma ba.

A karkashin tsarin, za a samar da katafaren gonaki na zamani da za a rika sarrafa nama, nono da dangoginsa ta hanyar amfani da na’urori na zamani.

Mataimakin shugaban kasar ya yi fatan cewa shirin zai taimaka wajen wararen rikice-rikicen manoma da makiyaya.

Tags:
Comments(0)