Netanyahu Ya Gudu Zuwa Maboya Saboda Makamai Masu Linzami

2019-09-11 08:55:21

Pira Minista HKI Ya Gudu Zuwa Maboya Saboda Makamai Masu Linzami Da Palasdinawa Suka Harba Daga Gaza

Kafafen watsa labarun HKI sun ce; Benjamin Netanyahu ya katse jawabin yakin neman zabe da yake yi a garin Usdud, inda ya gudu zuwa maboya , bayan kadawar jiniya saboda harbo makamai masu linzami da Palasdinawan yankin Gaza su ka yi.

Tashar talabijin dan hki ta channel 11 ta nuna hoton yadda jami’an tsaro suka fitar da Pira minista Netanyahu daga cikin dakin taron yakin neman zaben.

An ji karar jiniya a cikin garuruwan usdud da Asqlan da suke kusa da yankin Gaza, domin fadakar da mutane akan makamai masu linzamin da aka harbo zuwa cikin garuruwan da ‘yan Sahayoniya su ka mamaye.

Wasu kafafen watsa labarun sun ce’ makamai masu linzami biyar ne palasdinawa su ka harba daga Gaza.

Tags:
Comments(0)