Shugaban Amurka Ya Kori Mai Ba Shi Shawara Akan Harkokin Tsaro

2019-09-11 07:37:55

Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta bayar da labarin cewa; shugaban kasa Donald Trump ya kori John Bolton daga aikinsa na mai bayar da shawara akan harkokin tsaron kasa.

Shugaban kasar ta Amurka Donld Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; A daren jiya na sanar da John Bolton cewa daga yanzu fadar White House ba ta bukatar aikinsa. Ni da wasu jami’an gwamnati muna da sabani mai tsanani akan wasu shawarwarin da yake bayarwa, don haka na bukaci John din da ya gabatar da takardar yin murabus dinsa da safe. Ina godiya ga John saboda hidimar da ya yi. A mako mai zuwa zan gabatar da sabon mai bayar da shawara ga harkokin tsaron kasa.”

Tun tuni dai kafafen watsa labarun Amurka suke ambaton sabanin da ake da shi a tsakanin shugaban kasar da mai ba shi shawara akan al’amurra da dama.

A baya Donlad Trump ya fadi cewa; Da ace yana aiki da shawarwarin John Bolton, to da tuni kasar Amurka ta fada cikin yaki mai tsanani.

Tags:
Comments(0)