Miliyoyin Mutane Sun Gudanar Da Juyayin Ashura A Iran

2019-09-10 17:57:02

Miliyon mutanen kasar Iran ne a duk fadin kasar suka gudanar da juyayin Ashoora a yau talata, don raya ranar shahadar Imam Husain (a) jikan manzon Allah (s) wanda ya yi shahada a ranar 10 ga watan Muharram na shekara ta 61 hijira kamariyya.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto cewa an gudanar da makokin Ashoora a nan Tehran da sauran birane da garuruwan kasar kamar yadda aka saba a ko wace shekara.

Har’ila yau an gudanar da iran wannan juyayin a Husainiyar Imam Khomaini(q) inda jagoran juyin juya halin musulunci Aya Sayyeed Aliyul ya sami halattarsa a gidansa a nan birnin Tehran.

Banda haka an gudanar da irin wannan juyayin a kasashen duniya da dama wadanda suka hada da hubbarin Imam Husain (a) wanda yake birnin Karbala a kasar Iraqi.

Raya wannan ranar, da kuma juyayi yana daga cikin muhimman lamura wadanda limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s) suka kodaitar ga mabiyansu.

Tags:
Comments(0)