Nasarallah: Yaki Da Iran Zai Zama Karshen Isra'ila

2019-09-10 17:54:06

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasarallah ya bayyana cewa kungiyarsa tana kashedi wa manya-manyan kasashen duniya dangane da duk wani kokarin na farwa JMI da yaki.

Shugaban kungiyar na Hizbullah ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a safiyar yau Talata wanda yayi dai-dai da ranar ashoora 10 ga watan Muharram na wannan shekara ta 1441H.K.

Sayyeed Nasarallah ya kara da cewa duk wani yakin da za’a kaiwa kasar Iran kamar kunna wutar yaki ne a yankin gaba daya.

Nasarallah ya kara da cewa kungiyar ba zata zama yar kallo ba a duk lokacinda aka farwa kasar Iran da yaki.

Daga karshe Sayyeed Nasarrala ya kamma da cewa duk wani yakin da za’a fadawa kasar Iran da shi, zai zama sababin shafe HKI daga doron kasa, sannan zai kawo karshen samuwar sojojin Amurka a yankin gaba daya.

Tags:
Comments(0)