​Firai Ministan Kasar Aljeriya Zai Ajiye Aikinsa

2019-09-10 17:39:03

Daga karshe Firai ministan kasar Algeriya Nuruddeen Bedui ya bada sanarwan cewa zai ajiye mukaminsa don share fagen gudanar da zabubbuka a kasar a cikin wannan shekara.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Firai Ministan yana fadar haka a yau Talata.

Labarin ya kara da cewa saukar firai ministan daga mukaminsa na daga cikin bukatun masu zanga-zanga tun watan Febreru na wannan shekara a kasar. A kokarinsu na ganin bayan tsohon shugaban kasar da kuma mukarrabansa kan madafun ikon kasar.

Kafin haka dai babban komandan sojojin kasar ta Algeriya ya bukaci hukumar zaben kasar ta bayyana ranar da za’a gudanar da zabe a kasar kafin ko kuma a ranar 15 ga watan satumba na wannan shekara don a gudanar da zabubbuka kafin karshen wannan shekara.

Tags:
Comments(0)