Taliban: Trump Zai Yi Nadamar Yin Watsi Da Yarjejeniyar Afghanistan

2019-09-10 17:29:49

Kungiyar Taliban ta kasar Afganistan ta bayyana cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump zai yi nadamar yin watsi da yerjejeniyar da Amurka ta cimma da ita a kasar Qatar.

Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid yana fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa, dama zabi biyu ne Amurka take da su ko tattaunawa da ita Taliban, wanda aka gudanar a kasar Qatar ko kuma dayan zabin wato yaki.

A jiya litinin ne dai shugaban kasar ta Amurka Donal Trupm ya bayyana cewa yerjejeniyar da gwamnatinsa ta cimma da kungiyar Taliban bayan tattaunawa mai tsawo a kasar Qatar a cikin yan kwanakin da suka gabata, ba a bakin kome yake ba a wajensa. Banda haka Trump ya ce sojojinsa zasu ci gaba da yaki mayakan kungiyar a kasar ta Afganistan.

Amurka dai tana mamaye da kasar Afganistan tun shekara ta 2001, wato shekaru 18 da suka gabata ke nan.

Tags:
Comments(0)