Ashirye muke muji bukatun malam jami’a

2018-11-07 14:07:26

Gwamatim tarayya ta shirya domin tattaunawa akan bukatun malaman jam’ia saboda gujewa shiga yajin aiki.

Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya bayyanawa manema labarai cewa, wannan matsalar ta kungiyar malaman jami’a ta fara ne tun mulkin marigayi shugaba Yar adua a shekarar 2009, sannan gwamnatin ta so ta biya musu bukatun su amma saboda karye war farashin mai ya sanya hakan bai yiyu ba.

Wannan karyewar farshin mai ya kawo cikas babba a cikin harkokin kasuwanci na kasa baki daya wanda ya kawo ci baya sosai a bangaren ilimi.

Ministan ya ci gaba da cewa, yanzu an samu sauyi na samun farfadowar farashin mai don haka lallai za'a samu gagarumar ci gaba a bangaren ilimi

Don haka ina mai jawo hankulan Iyayen yara da ma su kungiyar malamai da su kara hakuri za'a samu ci gaba nan ba da jimawa ba, kuma su sani cewa ba kwai bangaren ilimi bane ke da matsala akwai wasu bangarorin ma da suna bukatan kulawa na musamman.

Tags:
Comments(0)