Unicef Tayi Gargadi A Kan Mawuyacin Halin Da Ake Ciki A Al-Hudaidah Yamen

2018-11-07 13:49:15

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi gargadi akan halin da yara kanana suke ciki a Asibitocin da ke yanke Al-Hudaidah.

Unicef din ta bayyana cewa,da ga Asibitin Alsaura inda kimanin yara 59 ke kwance , zaka iya jiyo kararrakin abubuwa masu fashe wa da na manyan bindi wanda hakan ke kawo barazana ga rayukan yaran.

Unicef din ta kara da cewa, da zarar aka rufe hanyoyin isa Al-Hudaidah toh za'a iya hasarar rayuka masu dimbin yawa.

Tun bayan shekaru uku da suka wuce kasar Saudiyya tare da hadin kan 'yan kanzaginta suke kai hari kan al'ummar Yamen wanda haka yai sanadiyyar rasa rayuka da dama.

Tags:
Comments(0)