Amruka Zata Sake Kakafawa Rasha Takunkumi

2018-11-07 12:57:58

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amruka a jiya Talata ta sanar da cewa, ma'aikatar na zantawa da kwangire domin sakawa Rasha wasu sabbin takunkumi.

Kamar yadda Heather Nauert ta sanar cewa, wadannan sabin takunkumin za 'a kakafawa Rasha ne sabo da tace tana da hannu wajen sanyawa tsohon dan leken asirin Rasha wanda ke gudun hijira a Birtaniya guba.

Sergei Skripal tsohon dan leken asirin Rasha da ke Birtaniya an shakar da shi iska mai guba tare da iyalinsa, kuma jami'an tsaron Birtaniya sun tabbatar da afkuwar hakan.

Sai da kasar Rasha ta karyata dukkan wata tuhuma da ake mata na tana da hannu a afkuwar lamarin.

Tags:
Comments(0)