Jamus Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Hulda Da Iran

2018-11-07 12:52:00

Jakadan Jamus a Iran yace, takunkumin Amruka akan Iran ya sabawa doka, saboda haka kasarsa zata ci gaba da hulda da jamhuriyyar musulunci.

Michael Klor-Berchtold jakadan jamus a Iran a ya yin da yake ganawa da mataimakin ministan masana'antu da kasuwanci na Iran, ya sokin bakar siyasar Amruka akan Iran ya kuma ce kasarsa zata ci gaba da girmama yarjejeniyar shirin Iran na makamashin nukiliya na zaman lafiya.

Jakadan ya kara da cewa , Berlin na neman hanyar da zata saukakawa kamfanonin Iran samun bizar shiga kasar Jamus domin su baje kolin su a kasuwar baje koli wadda zata gudana a Jamus.

Tags:
Comments(0)