Duniya Na Juyayin Wafatin Fiyayyen Halitta

2018-11-07 12:30:52

28 ga watan safar shekara 11 bayan hijirar Manzon Allah{ s.a.w.w} Fiyayyen halitta Annabin Rahama ya bar wannan Duniyar , ya yi wafati yana da shekaru 63 a Duniya.

Wafatin Manzon Rahama mai tsira da aminci ya zo dai dai da shahadar jikansa kuma Imami na biyu a cikin jerin Imaman tsira wato Imam Hassan Mujtafa{a.s}.

Duniyar musulmi na cikin juyayi da nuna alhini na wafati Annabin Rahama Muhammad Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi, sai kuma alhinin shahadar Imam Hassan Mujtafa{a.s}.

muna taya al'ummar musulmi juyayin zagayowar wannan rana.

Tags:
Comments(0)