Buhari Ya Aminci Da 30,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi A Nageria

2018-11-06 21:15:07

Shugaba Muhammdu Buhari ya amince da biyan Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

Buhari ya amince da wannan bukatar bayan ruhotannin da kwamitin bincike kan tantance albashi suka gabatar masa a fadarsa dake Abuja.

Za'a aika da wannan yarjejeniya zuwa ga Majalissar tarayya ta kasa domin canza mafi karancin albashi daga Naira 18,000 zuwa Naira 30,000.

Tags:
Comments(0)