An Dage Ganawa Da Za'ayi Tsakanin Putin Da Trump

2018-11-06 21:08:49

Kakakin fadar shugaban kasar Rasha yace, an samu canji a ganawar da aka shirya yi tsakanin shuwagabannin Rasha da Amruka a kasar Faransa.

Kakakin yace, ba wani abune ba ya kawo cikas wajen ganawar ba, sai dai bikin tunwa da kawo karshen yakin Duniya na daya.

Ya kara da cewa, shirye shiryen bikin ne wanda aka shirya a Faransa ya cinye lokacin, amma dai shuwagabanin zasu samu damar gai sawa da juna.

A satin da ya wuce ne aka shelanta ganawar shuwagabanin biyu a taron Faransa.

Tags:
Comments(0)