Macron Ya Bukaci Tarayyar Turai Da Ta Kafa Runduna Mai Karfi

2018-11-06 20:21:38

Shugaban kasar Faransa ya bukaci tarayyar turai da ta kafa runduna ta tsaro wadda bata dogara da Amruka.

Emmanuel Macron shugaban kasar Faransa a jiya Talata a ya yin hira da Radiyo Europe 1 yace, dole ne kasashen tarayyar turai ya zamanto suna da runduna ta tsaro mai matukar karfi.

Shugaban ya kara da cewa, a cikin wannan yana yin da ake ciki muna da matukar bukata ga runduna mai karfi ta yadda zamu iya kare kan mu.

Ya kuma ce, dole ne turai ta samar da tsari na tsaro wanda ya sha bamban da na Amruka.

Tags:
Comments(0)