An Bukaci Da A Tsuke Bakin Aljihu A Lokacin Gudanar Da Zabuka A Nageria

2018-10-11 12:58:11

Majalisar tarayya a Nageria ta bukaci da a tsuke bakin aljihu a lokuttan gudanar da zabuka shekara ta 2019.

wakilan Majalisar tarayya a Nageria sun yi kira da cewa, kudaden da ya kamata a kashe a ya yin gudanar da zabe shugaban kasa kada su haura biliyan 5 kamar yadda kundin dokar kasar ya tana da.

Sun kuma ce zaben Gwamnoni kada a kashe sama da biliyan 1 na 'yan Majalissu kuma ka da ya wuce Naira miliyan 100.

Almubazziranci da kudi a ya yin gudanar da zabuka a Nageria ba wani bakon abu ba ne.

Tags:
Comments(0)