Kimanin Mata Dubu Uku Ne Suka Rasa Rayuka Tun Farkon Fara Yakin Yamen

2018-10-11 12:55:49

Ma'aikatar lafiya ta Yamen ta sanar da cewa da ga lokacin da Kasar Saudiyya ta kaddamar da hari akan Yamen ya zuwa yau kimanin mata 3000 ne suka rasa rayukan su.

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya shelanta cewa, tun farkon fara kai hare-hare da hadakar Saudiyya suka kaddamar a Yamen kimanin yara 5000 ne suka rasa rayu kan su ya zuwa yanzu.

Harin da Saudiyya tare da goyon bayan Amruka suke kai wa a Yamen da ga shekara ta 2015, ya janyo rasa rayuka dubu goma sha hudu, da kuma hasarar dukiya mai yawa.

Tags:
Comments(0)