Amruka Na Yiwa Kasashen Duniya Barazana A Kan Sayen Man Fetur Din Iran

2018-10-11 12:52:46

Shugaban kasar Amruka ya gargadi kasashen da ke da niyyar sayen man fetur din Iran bayan takunkumin da aka kakafawa kasar da cewa su kuka da kan su.

Donald Trump ya yin da yake amsa tambayoyin manema labarai dan gane da cigaba da sayen man fetur din Iran da wasu kasashe irin su Chana da Indiya ke alhalin Amruka da haramta sayen man fetur din da ga Iran, Trump ya amsa da cewa, "muna nan mun san yawa irin wadannan kasashe ido".

Amruka ta ficce da ga yarjejeniyar da a ka rattabawa hannu ta shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya a cikin watan mayu, idan kuma ta sabuta takunkumin hana sayen danye man fetur din Iran.

Tags:
Comments(0)