Ana Tsare Da Matan Palastinawa Sama Da 90 A Gidajen Yari Na HK,Isra'ila

2018-10-11 12:50:37

A farkon shekarar 2018, jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun kama sama da mata 90 kuma suke tsare su a gidajen yari daban daban.

Taskar watsa labarai ta pars-today ta nakalto cewa, cibiyar da ke kula da hakkokin 'yan gida yari da kuma kare hakkin bil'adama wacce ake kira da suna {Aldhamir} ta fitar da wata sanar wa wadda ke nuni da cewa, a cikin watannin da suka gabata jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun kama matan Palastinawa 51 wanda 2 da ga cikin su yara ne sai kuma wasu 9 na da ciwu ka a jikin su.

Cibiyar ta ce, da ga farkon wannan shekarar ta 2018 zuwa yau jami'an tsaron sun kama kimanin matan Palastinawa 90.

Tags:
Comments(0)