Birtaniya Na Neman Fadada Hulda Da Iran

2018-10-11 12:48:38

Jakadan Birtaniya a Tehran a wata ganawa da ya yi da 'yan kasuwar Iran ,yace kasar sa na bukatar fadada hulda kasuwanci da Iran.

"Rob Macaire" jakadan kasar Birtaniya a Tehran ya kai ziyarar aiki a garin Yazd idan ya yi wata ganawa da 'yan kasuwar garin. jakadan ya ce masu kasar Birtaniya na bukatar samar da wani tsarin Banki na musamman wanda zai tai maka waje kulla hulda cinikayya tsakani Iran da kasashe Turai.

Ya kara da cewa, karfafa hulda tsakanin kamfanoni Iran da na Birtaniya zai tai maka wajan samar da kyakyawar alaka a tsakanin kasashen biyu.

Tags:
Comments(0)