Mataimakin ministan harkokin wajen Iran yace, jamhuriyyar muslunci ta Iran na kan sahun gaba wajen yaki da ta'addanci da kuma fasa kwaurin miyagun kwayoyi.
Ghulam Ali Dehghani a jiya Laraba ya shedawa manema labarai cewa, idan aka yi la'akari da salon siyasar makiya jamhuriyyar muslunci ta Iran na kokarin kawo tashe-tashen hankula,shigar da miyagun kwayoyi a cikin matasa da sauran makirce-makirce.
mataimakin ministan ya kara da cewa, yana da kyau makiya su sani cewa, kasar Iran na kan sahu na gaba wajen yaki da ta'addanci da kuma fasakwaurin miyagun kwayoyi a duniya.