Nageria: Ba Za'a Tsige Dogara Ba-Cewar Wani Dan Majalisa

2018-10-10 17:51:15

Babban wakili a majalisar wakilai Alhassan Doguwa ya karya ta jita-jitar game da yi yuwar cire shugaban majalisa Yakubu Dogara da ga kujerar sa.

Dogara wanda yai canjin sheka da ga jama'iyar APC mai mulki zuwa jama'iyar PDP mai adawa, ya na fuskantar barazanar tsigewa kamar yadda Bakula Saraki ya fuskanta a baya.

Bayan komawar tasa a jama'iya PDP an ta kiranye akan dole Dogara yau sauka kan kujerarsa ko kuma a tsige shi, kamar yadda a ka fadawa Saraki a baya.

Doguwa yace Yakubu Dogara na da 'yanci zaba wa kansa duk jama'iyar da ya ke so.

Tags:
Comments(0)