An Yada Sunaye Da Kuma Hotunan Wadanda A Ke Zargi A Kan Batan Kashoogi

2018-10-10 17:43:02

Kafafen yada labarai na Turkiya sun yada sunaye da kuma hotunan wasu jami'an Saudiyya 15 wadanda a ka tabbatar da sun shiga karamin ofishin jakkadanci Saudiyya a Istanbul a dai dai ranar da Kashoogi ya bata.

Kafafen watsa labarai na Turkiya sun yada sunaye da kuma hotunan wasu jami'an kasar Saudiyya 15 da suke je Istanbul kuma suka shiga karamin ofishin jakkadanci Saudiyya da ke a Istanbul din a dai dai ranar da shahararren dan jaridar nan wato Jamal Kashoogi ya yi batan dabo.

Kafafen watsa labaran na zargin wadannan mutane 15 da azaftar wa da kuma kisan Kashoogi.

Kashoogi ya dai shiga karamin ofishin jakkadanci Saudiyya ne da ke Istanbul domin gudanar da wasu bukata da suka taso masa wanda hakan yasa ya baru Amruka inda yake da zama, amma kuma har ya zuwa yanzu ba wanda ya sake jin duriyar sa.

Tags:
Comments(0)