Nijeriya: Ba A Samu Mutuwa Ba Cikin Kwanaki 6 Da Suka Gabata Saboda COVID-19

2020-11-21 14:52:42
Nijeriya: Ba A Samu Mutuwa Ba Cikin Kwanaki 6 Da Suka Gabata Saboda COVID-19

A wani abu da ake ganinsa a matsayin ci gaba a fadar da ake yi da cutar nan ta COVID-19 ko kuma Coronavirus a Nijeriya, rahotanni daga kasar sun ce cikin kwanaki 6 cikin bakwai din da suka gabata ba a samu mutuwa ko da guda ba saboda cutar ta COVID-19.

Rahotannin sun ce bisa ga kididdigar da hukumar kula da cuttuttuka ta kasar NCDC take fitarwa a kullum dangane da wadanda suka kamu da cutar ta korona da kuma wadanda suka rasa rayukansu ko kuma suka warke, ba a samu wani da ya mutu saboda cutar ba cikin kwanaki shida cikin bakwai na satin da ya gabata ba.

Rahotannin sun kara da cewa mutuwa uku kacal kawai aka samu a duk fadin kasar tsawon kwanaki takwas din da suka gabata daga cutar ta Korona.

Ya zuwa yanzu dai mutane 1,165 ne suka mutu sakamakon cutar a Nijeriya. Sannan adadin wadanda suka kamu da ita kuma sun kai mutane 65,982 wanda hakan ya sanya Nijeriya ta zama kasa ta biyar a Afirka cikin jerin kasashen da suke kan gaba da kamuwa ta cutar bayan kasashen Habasha, Masar, Moroko da kuma Afirka ta Kudu.

014

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!