Dakarun Yemen Sun Kwace Wani Sansanin Soji Mai Muhimmanci A Lardin Ma’rib

2020-11-21 14:47:55
Dakarun Yemen Sun Kwace Wani Sansanin Soji Mai Muhimmanci A Lardin Ma’rib

Dakarun kasar Yemen da suke samun goyon bayan dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar kwace ikon wani sansanin soji mai matukar muhimmanci da ke lardin Ma’rib da ke tsakiyar kasar bayan wani gumurzu da suka yi da sojojin sa kai da Saudiyya ta ke goya musu baya wadanda kuma suke biyayya ga tsohon shugaban kasar Abd Rabbuh Mansur Hadi.

Kafafen watsa labaran kasar ta Yemen sun ba da rahoton cewa sojojin kasar Yemen din da dakarun sa kai masu goya musu baya sun kwace da kuma tabbatar da ikonsu sansanin sojin na Maas mai matukar muhimmanci bayan gumurzun da suka yi da masu dauke da makami da suke da alaka da kungiyar ta’addancin nan ta Al-Qa’ida da suke da alaka da kungiyar Salafish Islah Party.

Shi dai wannan sansanin yana nan ne kimanin kilomita 57 daga babban birnin lardin Ma’rib din, kuma shi ne babban sansanin soji da ‘yan bindiga dadin suke da shi.

Wannan dai babbar nasara ce da dakarun Yemen din da masu goya musu baya suka samu a kokarin da suke ci gaba da yi na kare kasar daga wuce gona da irin Saudiyya da kawayenta sama da shekaru biyar da suka gabata da yayi sanadiyyar mutuwar dubun dubatan al’umma kasar da kuma sanya wasu miliyoyi cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

014

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!