Shugaban Venezuela Ya Sanar Da Fara Kera Jiragen Sama Marasa Matuka Da Kuma Kananan Jirage A Kasar

2020-11-21 14:44:36
Shugaban Venezuela Ya Sanar Da Fara Kera Jiragen Sama Marasa Matuka Da Kuma Kananan Jirage A Kasar

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya sanar da cewa kasarsa ta kaddamar da fara kera jiragen sama marasa matuka da kuma wasu kananan jiragen sama da za su iya gudanar da ayyuka daban-daban cikin shirin kasarsa ta tabbatar da tsaron kasar.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan da shugaba Maduron ya sanya hannu kan wata doka da ta kafa Cibiyar kasa ta zirga zirgar jiragen sama wadanda aka dora wa alhakin tsarawa, kerawa da kuma gyaran sabbin kanana jiragen sama da kuma jirage marasa matuka da za a dinga kerawa a cikin gida.

Shugaba Maduro ya ce an tsara wannan shiri ne duk da nufin tabbatar da ci gaban kasar da kuma tabbatar da tsaronta.

A watan Satumban da ta gabata ma dai shugaba Maduron ya ba da umurnin kafa wata majalisar soji da nufin gudanar da ayyukanta kan samar da makaman da kasar take bukata duk kuwa da irin takunkumin da take fuskanta.

Kasar Venezuelan dai tana fuskantar takunkumi mai tsanani da kuma barazanar kawo mata harin soji daga Amurka baya ga kokarin da gwamnatin Amurka take ci gaba da yi na ganin ta kifar da gwamnatin shugaba Maduron amma dai lamarin ya ci tura.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!