WHO : Za’a Dau Dogon Lokaci Ana Fama Da Annobar Korona

2020-08-02 10:04:30

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta bayyana cewa mai yiwuwa a dau lokaci mai tsawo ana fama da annobar cutar korona.

Wannan bayyanin na kunshe ne a sanarwar da kwamitin gaggawa na hukumar ya fitar a taronsa karo na hudu a Geneva, domin duba halin da ake ciki game da cutar.

Bayyanin na WHO, na zuwa ne a daidai lokacin annobar ke ci gaba da yaduwa a duniya.

Ye zuwa jiya Asabar, adadin mutanen da cutar ta yi ajalinsu a fadin duniya, tun bayan bullarta a watan Disamban bara su kai akalla dubu 680 a cewar alkalumman kamfanin dilancin labaren AFP.

Yawan kuma wadanda cutar ta harba, a cikin kasashe da yankuna 196 na duniya sun haura miliyan 17 .

Saidai a cewar AFP, wannan alkalumman kalilan ne akan ainahin yawan mutanen da suka harbu da cutar, saboda a wasu kasashe akan yin gwajin cutar ne kawai ga wadanda ke cikin mayuyacin hali.

Kasashen da cutar ta fi wa illa a cikin alkalumman baya baya nan sun hada da Amurka inda mutum (1.442) suka mutu, sai Brazil (1.212) da kuma Indiya (764).Tags:
Comments(0)