Libiya : Takun Saka Tsakanin Turkiyya Da Hadaddiyar Daular Larabawa

2020-08-02 10:02:52

Ana ci gaba da samun takun-Saka tsakanin kasashen Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa kan batun kasar Libiya dake fama da yaki.

Takun tsakan ya yi zafi a baya baya nan inda Hadaddiyar Daular Larabawa ta bukaci Turkiyya data shiga tafiye tafiyenta ta kuma tsame hannunta a cikin harkokin kasashen Larabawa.

Kafin hakan dai a ranar Juma’a data gabata, Turkiyya, ta bakin ministan tsaronta ta soki ayyukan kasar ta Hadaddiyar daular Larabawa a Libiya.

Kasashen biyu dai na mara baya ga bangarori biyu dake rikici da juna a kasar Libiya, da suka hada da gwamnatin hadin kan kasa ta Fayez Al-Saraj dake samun goyan bayan MDD, da kuma ta Marshal Khalifa Haftar dake rike da ikon gabashin kasar.

Baya ga kasashen Turkiyya da Hadaddiyar daular Larabawa akwai kasar Masar dake goyan bayan Haftar, wacce kwanan baya ta yi barazanar aikewa da sojoji a Libiyar dake fama da yaki.

Libiya dai ta fada cikin rudani ne tn bayan kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Mirigayi Mu’ammar Ghaddafi a cikin shekarar 2011.

Tags:
Comments(0)