Afrika Ta Kudu Ta Samar Da Na'urorin Taimakon Numfashi

2020-08-02 10:01:30

Kasar Afrika ta Kudu ta kammala kashi na farko na kera na'urorin taimakon numfashi, wadanda za su taimaka mata yaki da cutar COVID-19.

Ministan ciniki da masana'antu na kasar Ebrahim Patel ne ya bayyana haka, yayin wani taro kan COVID-19. Inda ya ce, an kammala harhada na'urorin, wanda wani bangare ne na guda 10,000 da aka yi oda da farko, da cibiyar binciken kimiyya da masana'atu ta kasar ta kera.

Afrika ta Kudu na daga cikin kasashen dake sahun gaba wajen yawan masu fama da cutar, inda yanzu haka yawan wadanda aka tabbatar sun kamu sun haura rabin miliyan.

A watan Afrilun da ya gabata ne ta kaddamar da wani shiri na rand miliyan 250, kwatankwacin dala miliyan 14.7 domin samar da na'urorin a kasar.

Baki daya, shirin zai samar da naurori 20,000.

Tags:
Comments(0)