Ministan Tsaron Iran: Takunkumin Makiya Ya Kara Azamar Matasan Juyin Juya Halin Musulunci

2020-08-01 21:34:44

Ministan tsaron Iran Janar Amir Hatimi ne ya bayyana cewa; Ma’aikatar tsaro ta tabbatar da cewa takunkumin makiya bai yi tasiri akan azamar samarin kasar da masu kyakkyawan niyya ba wadanda su ka tabbatar da cewa aikinsu shi ne ‘yantar da kasa daga duk wani kokarin danniya na Amurka, da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta ta fuskar kera abubuwan da take bukatuwa na kayan tsaro.

A jawabin da ya gabatar a yau Asabar, ya yi ishara da jawabin jagoran juyin musulu nci mai cike da hikima wanda ya yi jinjina akan wadanda su ka kera jirgin bayar da horo na “kauthar”, sannan ya kara da cewa; Jawabin yana kara cusa fata a cikin zukatan masana da sauran al’ummar Iran.

Har ila yau, ministan tsaron na Iran ya bayyana nasarorin da aka samu na kere-kere ta fuskar tsaro a cikin Iran daga ciki hadda makamin “Babar 373” na bayar da kariya ta sararin samaniya, da sauran makamai masu linazami samfurorin Cruise da Balastic da jirgin ruwa na yaki mai ninkaya a karkashin ruwa.

Tags:
Comments(0)