​China Tana Daukar Matakan Rage Haihuwa A Tsakanin Musulmin Kasar

2020-06-29 20:31:56

Gwamnatin kasar China na daukar tsauraran matakan tilasta wa ‘yan kabilar Uyghur da wasu tsiraru rage haihuwa da zimmar dakile yawan al’ummar Musulmi a kasar.

Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta China tana daukar wadannan matakai nea akn musulmi, a daidai lokacin da kuma take karfafa gwiwar ‘yan kabilar Han kan su ci gaba da kara haihuwa.

A lokutan baya daidaikun mata sun yi korafi game da tilasta musu takaita haihuwa, kuma wannan tilastawar ta kara tsananta a halin yanzu.

Kamfanin dilalncin labaran Associated Press wanda fitar da wannan rahoto, ya tattara alkalumansa ne ta hanyar amfani da kididdigar hukumomi da wasu bayanai na gwamnati, da kuma hirarrakin da ya yi da mutanen da aka tsare su a wani sansani, saboda kin bin tsarin rage haihuwar.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyoyin kare hakkin bil adama a duniya sun yi ta zargin gwamnatin kasar China da gallaza wa musulmi, ta hanyar kame su da tsare a gidajen kaso, saboda saba wa ka’idojin da gwamnatin kasar take gindayawa, wadanda musulmi suke ganin sun yi karo da addinin, musamman hana musulmi yin azumi a cikin watan Ramadan a wasu yankunan kasar, da kuma hana matan musulmi haihiwa, da ma wasu ka’idojin da gwamnatin China ke zargin musulmin ba su biyayya a kansu.

Tags:
Comments(0)