​Nakhala: Ha’incin Gwamnatocin Larabawa A Kan Falastinu Ya Fi Muni A Kan Mamayarta

2020-05-23 10:13:29

Shugaban kungiyar Jihadul Islami Ziyad Nakhala ya yi gargadi dangane da ha’incin wasu kasashen larabawa dangane da batun Quds da Falastinu.

Tashar al’alam ta bayar da rahoton cewa, a zantawar da ta yi da babban sakataren kungiyar jihadul Islami Ziyad, ya bayyana cewa, babbar matsalar da ake fuskanta a halin yanzu ita ce, wasu daga cikin gwamnatocin kasashen larabawa suna hada baki da Isra’ila wajen cutar da al’ummar Falastinu, wanda hakan a cewarsa ya fi muni a kan mamaye Falastinu.

Ya ce abin ban takaici ne yadda wasu daga cikin ‘yan uwansu larabawa ne da kansu suke yin aiki tare da yahudawa babu dare babu rana wajen cutar da al’ummar Falastinu, tare da halasta wa yahudawa mamayar yankunan muslmi a Falastinu, daga ciki har da masallacin quds mai alfarma.

Nakhala ya ce; abin da Iran ta yi dangane da batun Falastinu ya isa abin alfahari ga dukannin falastinawa da larabawa da ma musulmi baki daya, inda ba ta boye ma duniya ba kan taimakon da take baiwa al’ummar falastinu, kuma ita ce kan gaba wajen kare duk wani abu da ya shafi Falastinu a duniya.

Baya ga haka ya kara da cewa, dukkanin matsin lamabar da Iran take fuskanta daga kasashe masu girman kai naduniya da takunkuman da suke kakaba mata, duk hakan sakamako ne na goyon bayan al’ummar Falastinu, da kuma sukar Isra’ila kan zaluncin da take yi kan Falastinawa.

Tags:
Comments(0)