​Yemen: Musulmi Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Al’ummar Falastinu

2020-05-23 09:56:58

Kwamitoci da kungiyoyin musulmi a kasar Yemen sun fitar da bayanai a kan ranar Quds.

Shafin yada labarai na Afaq ya bayar da rahoton cewa, kwamitoci da kungiyoyin musulmi a Yemen sun fitar da bayai da ke yin kira zuwa ga taimakon al’ummar Falastinu.

Bayanan sun mayar da hankali ne kan ci gaba da mamayar yankunan Falastinawa da Isra’ila ke ci gaba da yi, tare da jaddada wajabcin daukar matakai na taka ma Isra’ila birki kan hakan.

Haka nan kuma bayanan sun nuna takaici kan yadda wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa suka zama abokan kawance da Isra’ila wajen kitsa makirci akan al’ummar Falastinu.

Daga karshe musulmin na Yemen sun jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin kasashen larabawa da na musulmi kan batun Falastinu, da kuma daukar matakai na bai domin taimakon Falastinawa.

Tags:
Comments(0)