​Malawi: Shugabar Hukumar Zabe Ta Yi Murabus Daga Kan Mukaminta

2020-05-23 09:53:57

Shugabar hukumar zaben kasar Malawi ta yi murabus daga kan mukaminta, sakamakon fargabar abin da zai biyo baya, a zaben da za a sake gudanarwa a kasar, bayan rusa wanda ya gudana.

Shugabar hukumar zaben kasar Malawi Jane Ansah ta fuskanci matsaloli sakamakon dambaruwar siyasar kasar a farkon wannan shekara bayan da kotu ta rusa zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan Mayun shekara ta 2019 da ta gabata, inda hukumar zaben ta shelanta shugaba mai ci Peter Mutharika a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun kundin tsarin mulkin kasar Malawi ta sanar da cewa: Bincike ya tabbatar da zargin da 'yan adawar siyasar kasar suka gabatar cewa an tafka magudi a lokacin zabe.

Jaridar The Nation ta kasar Malawi ta watsa labarin cewa: Shugabar hukumar zaben kasar Jane Ansah ta yi furuci da cewa: Babu tabbas kan gudanar da sabon zabe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar.

Kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin dan-Adam sun gudanar da zanga-zanga a tsakanin watan Yulin shekara ta 2019 zuwa watan Janairun wannan shekara ta 2020, suna kira ga Ansah da sauran kwamishinonin hukumar zaben Malawi da su yi murabus daga kan mukamansu bayan dora alhakin magudin da suke zargin an tafka a lokacin zaben a kansu.


Tags:
Comments(0)