​Tarayyar Turai Ta Yi Kira Da A Dauke Wa Iran Takunkumai

2020-03-26 10:28:00
​Tarayyar Turai Ta Yi Kira Da A Dauke Wa Iran Takunkumai

Babban jami’in kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar, ya isar da kira ga mambobin kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki duniya, da su janye duk wani takunkumi na tattalin arzikia kan Iran.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya habarta cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron kungiyar kasashen G7 ta hanyar hoton bidiyo, Josep Borrell, Babban jami’in kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar, ya bayyana cewa dole ne a janye takunkuman da suke kan Iran, bisa la’akari matsalar cutar corona da ta addabi kasar.

Ya ce babu wani dalili da zai sanya a ci gaba da daukar matakai na matsin lamba a kan kasar Iran a cikin irin wannan yanayi, kuma a cewarsa tarayyar turaia shirye take ta maya baya domin ganin bankin duniya ya bayar da rancen kudade ga Iran da kuma Venezuella domin gudanar da ayyuka na musamman wajen yaki da cutar corona a cikin kasashen kasashensu.

Tags:
Comments(0)