​Kenya: An Kafa Dokar Hana Fitar Dare A Dukkanin Birane

2020-03-26 10:26:03
​Kenya: An Kafa Dokar Hana Fitar Dare A Dukkanin Birane

Gwamnatin kasar Kenya ta kafa dokar hana fitar dare a dukkanin biranen kasar, da nufin ganin an hana yaduwar cutar corona a cikin kasar.

Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ne ya kafa dokar ta hana fitar dare, baya ga haka kuma ya sanar da rage albashinsa da kuma zabtare haraji domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, Kenyatta yace daga ranar Juma’a mai zuwa kowa zai zauna a gida daga karfe 7 na dare zuwa karfe 5 na asuba, amma banda ma’aikatan lafiya da kuma wadanda ayyukansu suka zama dole.

Haka nan kuma Kenyatta ya bayyana shirin rage haraji ga mutanen dake karbar albashi kasa da Dala 226, yayin da ya bayyana cewa gwamnati ta saka dala miliyan 94 domin kula da dattijai da marayu da mabukata, domin rage musu matsaloli na rayuwa a cikin wannan mawuyacin hali.

Kenyatta dai rage kimanin kashi 80% na dukkanin albashin da yake dauka a cikin wata guda, domin gwamnati ta yi amfani da kudin wajne gudanar da ayyukanta da suka zama larura, kamar yadda kuma ya rage kashi 30% na albashin dukkanin ministocin kasar.

Tags:
Comments(0)