​Trump Ya Sanar Da Dokar Ta Baci Kan Corona A Jihohin New York, Texas, Florida

2020-03-26 10:13:19
​Trump Ya Sanar Da Dokar Ta Baci Kan Corona A Jihohin New York, Texas, Florida

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da dokar ta-baci kan corona a jihohin New York, Texas da kuma Florida.

Trump ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya saba gudanarwa a kowace rana kan corona a fadar White House da ke Washington, inda ya bayyana cewa, wadannan jihohi uku su ne suka tasirantuwa da cutar ta corona fiye da sauran jihohin kasar Amurka.

Ya ce cutar corona tafi yin illa a jihar New York fiye da kowace jiha a cikin Amurka, a kan haka gwamnatinsa na yin shiri na musamman domin taimaka wa jihar New York wajen shawo kan yaduwar wannan cuta.

Haka nan kuma Trump ya ce ga dukkanin alamu lamurra za su kara rincabewa a cikin makonni masu zuwa a kasar Amurka ta fuskar kara yaduwar cutar ta corona, inda ya ce akwai yiwuwar zai sake komawa majalisa domin neman amincewar majalisar kan taimaka ma bangarori na jama’a wadanda batun cutar ta corona ya cutar da su, ta hanyar rasa ayyukansu da shiga mawuyacin hali.

Gwamnan New ya sanar a jiya cewa, kimanin mutane 200 cutar corona ta kashe a jihar, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar a cikin jihar ta New ya kai mutane 17,856.

Hukumomin kiwon lafiya a Amurka sun ce mutane 69,008 ne suka kamu da cutar a fadin kasar baki daya, yayin da 1,045 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

Tags:
Comments(0)