Iran Ta Bukaci Tunisia Ta Goyi Bayan Kiraye-Kirayen Dagewa Kasar Takunkuman Tattalin Arzikin Amurka

2020-03-25 20:54:56
Iran Ta Bukaci Tunisia Ta Goyi Bayan Kiraye-Kirayen Dagewa Kasar Takunkuman Tattalin Arzikin Amurka

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya zanta da takwaransa na kasar Tunisia, Kais Sa’id, ta wayar tarko a daren litinin, inda ya bukaci gwamnatin Tunisia a matsayinta na mamba na wucin gani a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan yekuwar da ake yi na tilastawa gwamnatin Amurka dage takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Iran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, cutar Corona ta shafi kasashen duniya ne gaba daya, bai kamata kasashen duniya su zura ido suna ganin mutanen kasar Iran suna fama da wannan cutar ba tare da sun tallafa mata ba.

Shugaban Rauhani ya ce takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar suna hana ta yaki da cutar ta Corona, ya kuma kara da cewa yaki da wannan cutar yana bukatar hadin kan kasashen duniya, da kuma aiki tare a tsakaninsu don cimma wannan manufar.

A nashi bangaren shugaban kasar Tunisia Kais Sa’id ya yabawa JMI da irin kokarin da take yi a bangarori da dama, wadanda suka hada da yankin gabas ta tsakanin da kuma kasashen Musulmi.

Kais Sa’id, har’ila yau ya yi allawadai da takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Iran, sannan ya bukaci hadin kai da aiki tare a tsakanin kasashen duniya don kawo karshen takunkuman na zalunci.

Tags:
Comments(0)