Congo Ta Rufe Kan Iyakokin Kasarta Saboda Cutar Covid-19

2020-03-25 20:49:54
Congo Ta Rufe Kan Iyakokin Kasarta Saboda Cutar Covid-19

Gwamnatin kasar Congo ta bada sanarwan rufe kan iyakokin kasar saboda hana yaduwar cutar Covid-19 a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto shugaban kasar ta Congo Pelix Tshisekedi yana fadar haka a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa kasar ta shiga yaki da makiyin da ba’a ganinsa wanda kuma baya bukatar (Visa) ko izinin shiga wata kasa kafin ya shiga.

Shugaban ya hana Zirga-zirga daga ko’ina zuwa birnin Kinshasa babban birnin kasar. Ya kuma kara da cewa hanin ya shafi ta sama da kasa da kuma ruwa.

Banda haka shugaban ya hana taron mutane masu yawa sannan ya bukaci a rufe dukkan wuraren taruwar mutane wadanda suka hada da dakunan cin abinci da wuraren shan barasa da kade-kade.

A makon da ya gabata ne gwamnatin kasar ta Congo ta bada sanarwan kamuwar mutum na farko a kasar da cutar ta Covid-19, kuma ya zuwa jiya Talata adadin ya kai 45.

Kafin haka dai kasashen Afrika 45 su ka tabbatar da bullar cutar ta Covid -19 a kasashensu. Daga ciki har da kasashen Senegal, Najeriya da kuma Ivory Coast.

Tags:
Comments(0)