Daesh Ta Dauki Alhakin Kai Hare-Hare Kan Yanki Mai Arzikin Gas A Kasar Mozambik

2020-03-25 20:46:53

Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hare-hare a wani yanki a arewacin kasar Mozambique mai arzikin iskar gas a ranar Litinin din da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai hari ne kan garin Mocimboa na bakin ruwan tekun Indiya, inda aka gano dimbin arzikin iskar gas, sannan manya-manyan kamfanonin hakar iskar gas irin su Exxon Mobil da Total suke aiki.

Kakakin fadar shugaban kasar Mozambique, Filimao Suaze ya ce yan ta’addan sun kashe mutane da dama a garin, sun kuma lalata dukiyoyi masu yawa, sannan sun kwace iko da garin har zuwa safiyar jiya Talata a lokacin da jami’an tsaron kasar suka tilasta masu ficewa.

Tags:
Comments(0)