Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mabiya Addinan Hindu Da Sikh 200 A Kasar Afganistan

2020-03-25 20:41:38
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mabiya Addinan Hindu Da Sikh 200 A Kasar Afganistan

‘Yan bindiga wadanda har yanzun ba’a san ko su waye ba, sun yi garkuwa da mabiya addinin Hindu da Sikh tsiraru kimanin 200 a cikin dakin bautarsu a birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin gwamnatin kasar ta Afganistan Tariq Arian yana fadar haka a safiyar yau Laraba. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu jami’an tsaro sun killace yankin, sannan suna ta fafatawa da ‘yan bindigan don kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na “TOLO News”, na kasar ta Afganistan ya bayyana cewa ya sami labarin mutuwar mutane 10 da kuma jikkata wasu 10 a fafatawar da jami’an tsaron kasar suke yi da ‘yan bindigar.

Kafin haka dai kungiyoyin ‘yan ta’adda na Taliban da kuma Daesh ne suka saba yin irin wannan aikin.

Tags:
Comments(0)