Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Birtaniya Ya Kamu Da Cutar Corona

2020-03-25 20:38:55
Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar  Birtaniya Ya Kamu Da Cutar Corona

A dai-dai lokacinda cutar Corona take kara yaduwa a kasar Birtaniya, fadar Buckingham ta bada sanarwa a safiyar yau Laraba kan cewa yarima mai jiran gadon sarautar kasar Yerima Charles ya kamau da cutar Corona.

Majiyar muryar JMI daga birnin London ta bayyana cewa yarima Chales wanda ake wa lakabi da “yariman Whiles” ya kamu da cutar ne bayan yaduwarta daga wani mai taimkawa sarauniya Elizabeth na 2.

A halin yanzu dai Charles ya kebance kansa a wani wuri a yankin Scotland na kasar ta Birtania. Labarin ya kara da cewa matarsa Camilla, Duchess ba ta kamu da cutar ba, bayan an karbo sakamakon binciken.

Kasar Birtaniya dai tana daga cikin kasashen Turai da suka fi fama da cutar ta Corona a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

Har’ila yau sarauniya Elizabeth ta biyu tuni ta sauya wurin zamanta tun bayan bullar cutar a fadar Buckingham.

Tags:
Comments(0)