Dubban Yan Gudun Hijira Daga Kasar Kamaru Ne Suka Shiga Najeriya A Cikin Makonni Biyu Da Suka Gabata

2020-02-14 14:02:06

Fiye da yan kasar Kamaru 8000 suka shiga gabacin da kuma kudancin Najeriya a cikin makonni biyu da suka gabata saboda dirar mikiyan da jami’an tsaron kasar suka yi wa yankin masu Magana da harshen turanci.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar MDD daga birnin Geneva tana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa ya zuwa zaben gama garin da aka gudanar a karshen makon da ya gabata, yawan yan gudun hijira daga kasar Kamaru da suka shigo Najeriya sun haura 60,000.

Rikici tsakanin gwamnatin kasar Kamaru da kuma yan a ware na yankunan da ake Magana da turancin Ingilishi ya samo asali ne a lokacinda yan awaren, suka fara gwagwarmayan kafa kasarsu ta kansu mai suna Ambazonia don saboda wariyan da masu Magana da harshen faransanci, kuma masu rinjaye a kasar suke nuna masu.

Ya zuwa yaqnzu dai rikicin ya tilsatawa kimani mutane 500,000 kauracewa gidajensu a yankin.

Wannan rikicin shi ne kalu bale mafi girma wanda shugaban kasar ta kamaru Paul Biya yake fuskanta tun darewarsa kan kujerar shugabancin kasar shekaru 40 da suka gabata.

Tags:
Comments(0)