Kawancen Kasashe Masu Da'awar Yaki Da Daesh Ya Tabbatar Kisan Fararen Hula 1,370

2020-02-14 13:59:52

Sojojin kawance masu da’war yaki da kungiyar yan ta’adda ta Daesh a kasashen Siriya da Iraqi ya tabbatar da cewa daga watan Agustan shekara ta 2014 zuwa Disamban shekara ta 2019 sun kashe fararen hula 1,370 a kasashen biyu.

Majiyar muryar JMI ta nakalto kawancin kasashe masu da’war yaki da kungiyar Daesh yana fadar haka a jiya Alhamis, sannan ya kara da cewa wadannan kashe-kashen an yi su ne ba tare da nufin kisan fararen hula ba.

Labarin ya kara da cewa, binciken da wasu cibiyoyi masu zaman kansu suka yi dangane da kisan fararen hula a hare-haren da sojojin kawancen suke kaiwa a cikin kasashen biyu, ya nuna cewa fiye da fararen hula 8000 aka kasha.

An kafa kawanen kasashe masu da’awar yaki da kungiyar Daesh a kasashen Iraqi da Siriya ne a shekara 2014 tare da jagorancin kasar Amurka Sannan a tsakanin shekara 2014 zuwa 2019 sojojin kawancin sun kai hare-hare har sau 34,700 a cikin kasashen biyu.

Kasashen kawance masu da’war yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasashen Siriya da Iraqi dai sun hada da Amurka, kasashen Turai da wasu kasashen Larabawa. Amma kamar yadda ta bayyana a fili daga baya, wadannan kasashen ne suka samar da kungiyar ta Daesh don bawa kansu damar fadawa wadannan kasashe da yaki.

Tags:
Comments(0)