Algeria: Dole Ne A Maida Kasar Siriya Cikin Kungiyar Kasashen Larabwa

2020-02-14 13:56:53

Ministan harkokin wajen kasar Algeriya ya bukaci kasashen Larabawa su yi kokarin maida kasar Siriya cikin kungiyar kasashen.

Majiyar muryar JMI daga birnin Algies babban birnin kasar Algeriya ta nakalto Sabri Boukadoum, ministan harkokin wajen kasar yana fadar haka a jiya Alhamis.

Sabri Boukadoum ya kara da cewa rashin samuwar kasar Siriya a cikin kungiyar babbar asarace gareta. Don haka dole ne a yi kokarin maida ita cikin kungiyar.

A shekara ta 2011 ne dai kungiyar ta kasashen Larabwa, tare da matsin lambar kasashen yamma ta kori kasar Siriya daga kungiyar da sunan bukatar kifar da gwamnatin shugaba Bashar Al-Asad.

Amma tare da gagarumin nasarar da sojojin kasar ta Siriya suke samu kan yan ta’adda, wasu daga cikin kasashen larabawan sun soma sake bude ofisoshin jakadancinsu a birnin Damascua babban birnin kasar ta Siriya.

A halin yanzu dai sojojin kasar ta Siriya suna dab da kawo karshen ikon yan ta’addan ta Jibahatun Nusar, a lardin Idlib, tungarsu ta karshe a kasar ta Siriya.

Tags:
Comments(0)