Pakisatan Ta Nuna Damuwarta Da “Yarejejeniyar Karni”

2020-02-14 13:55:40

Gwamnatin kasar Paksitan ta bayyana yarjejeniyar karni wacce gwamnatin shugaban Trump na Amurka ta gabatar don warware rikicin gabas ta tsakiya a matsayin abin damuwa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto A’isha Farooqui kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan tana fadar haka a safiyar yau Jumma’a.

Farooqui ta kara da cewa shirin gwamnatin kasar Amurka na sayarwa kasar India makamai masu yawa, daga cikin har da garkuwan makamai masu linzami zai jefa kasashen yankin Asia ta kudu cikin rudani.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakistan ta bayyana haka ne, yan kwanaki bayan da wata kotu a birnin Lahor na kasar ta yanke hukunci daurin shekaru 5.5 kan Hafiz Sa’eed shugaban wata kungiyar yan ta’adda da ake kira Jama’atud Dawa da wasu mukarrabansa.

Dangane da dangantakar kasar Pakistan da Turkiya kuma Aisha Farooqui ta bayyana cewa dangantakar kasashen biyu tana da kyau, kuma ta yan’uwantaka ne da abokanai biyu.

Tags:
Comments(0)