​Najeriya: Kotun Koli ta tsige gwamnan jihar Bayelsa na jam’iyyar APC

2020-02-13 19:43:08

A hukuncin kotun kolin Najeriya wanda mai shari’a Ejembi Eko ya karanta, ya bayyana cewa dukkan Alkalai biyar da suka yi nazarin karar sun amince da wannan hukunci da kotun ta yanke.

Jaridar Premium Times ta bayar da rahoton cewa, dalilin tsige sabon gwamnan Lyon David na jam’iyyar APC shi ne samun mataimakinsa Bio Barakuma Degi-Eremienyo da laifin mika wa hukumar zabe takardun shedar kamala karatu na karya.

A dalilin haka Kotun ta bayyana cewa wannan matsala ta shafi gwamnan tun da shi ne ya mika shi a matsayin mataimakinsa a lokacin zaben gwamnan jihar.

Daga nan sai mai shari’a Eko ya umarci hukumar ta bayyana wanda ya zo na biyu a zaben gwamnan jihar, sannan a rantsar da shi ranar Juma’a.

Wannan hukunci na kotun koli bai yi wa jam’iyyar APC mai mulki a Najerya dadi ba, domin tuni shugaba Buhari ya shirya domin halartar bukin rantsar da gwamnan na Bayelsa wanda ya fito daga jam’iyyar ta APC, wanda hukumar zabe ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe.

Tags:
Comments(0)