​Ja’afari: Babu Batun Dakatar Da Bude Wuta A Idlib A Halin Yanzu

2020-02-13 19:16:31

Jakadan kasar Syria a majalisar dinkin duniya Bashar Ja’afari ya bayyana cewa, babu batun dakatar da bude wuta a Idlib a halin yanzu, tsakanin dakarun gwamnatin Syria da kuma mayakan ‘yan ta’adda da ke samun goyon baya dag akasashen ketare.

Ja’afari ya bayyana hakan ne a zaman da aka gudanar a kwamitin tsaron majalisar dinkin dinkin kan halin da ake ciki a yankin Idlib na Syria, wanda shi ne yankin daya tilo da ya rage a hannun ‘yan ta’adda a halin yanzu.

Ya ce, tun kafin wannan lokacin an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Rasha wadda ta girke dakarunta a cikin Syria bisa bukatar gwamnatin Syria, da kuma gwamnatin Turkiya wadda take mara baya ga kungiyoyin ‘yan bindiga masu yaki da gwamnatin Syria, kan dakatar da bude wuta a lardin Idlib.

Ja’afari ya kara da cewa, dakarun gwamnatin Syria sun dakatar da bude wuta alokacin, amma ‘yan ta’addan sun yi amfani da wannan damar domin kara karfafa kansu da kuma shigo da manyan makamai daga kasar Turkiya, kamar yadda ita ma Turkiya ta yi amfani da wannan damar domin jibge sojojinta a cikin Syria ba tare da izinin gwamnatin kasar ba.

Jakadan Syria a majlisar dinkin duniya ya ce Amurka da wasu kasashen turai ne suke yin amfani da Turkiya domin cimma manufofinsu na siyasa a kan Rasha da Syria, inda suke taimaka ma ‘yan ta’adda domin a ci gaba da zubar da jinin jama’a a Syria, amma ta hanyar yin amfani da gwamnatin Turkiya wajen aiwatar da hakan.

Tags:
Comments(0)